Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar COVID Ta Kashe Sama Da Mutum Dubu Uku A Najeriya – NCDC


Shugaba Buhari bayan da ya karbi rigakafin COVID-19 a karo na uku (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaba Buhari bayan da ya karbi rigakafin COVID-19 a karo na uku (Facebook/Bashir Ahmad)

A cewar hukumar ta NCDC, sabbin mutum 859 suka kamu da cutar a ranar Litinin da ta gabata.

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta ce mutum 3, 024 cutar coronavirus ta kashe tun daga lokacin da annobar ta barke zuwa yanzu.

NCDC ta bayyana hakan ne a kididdgar da ta fitar a ranar Litinin wacce ta bayyana iya adadin sabbin mutanen da aka gano suna dauke da cutar a ranar 27 ga watan Disambar 2021.

A cewar hukumar, sabbin mutum 859 suka kamu da cutar a ranar ta Litinin.

Daga cikin wannan adadi mutum 555 a jihar Legas aka same su, 57 a babban birnin tarayya na Abuja sai jihar Rivers mai mutum 44.

Sauran jihohin sun hada da Filato mai mutum 43 sai Edo mutum daya da Ondo mai mutum 34.

Kwara na da mutum 23 Kano 18, Ogun 16, Enugu 11, Oyo 6, Delta 5, Bauchi 3 sai Bayelsa mai mutum 3 ita ma.

Hukumar ta NCDC ta ce jimullar mutanen da aka gano cutar ta harba a kasar baki daya ta tsaya a dubu 238, 420 ya zuwa ranar Litinin.

XS
SM
MD
LG