Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Yunwa A Duniya Na Kara Kamari Yayin Da Manyan Kasashe Ke Rage Bada Tallafi


MDD
MDD

Lissafi ne mai sauki amma maras dadi. Yawan mutanen dake fama da yunwa ko ke fadi tashin rayuwa na kara karuwa a fadin duniya, a yayin da yawan kudaden da kasashe masu arziki ke bayarwa a matsayin gudunmowa da nufin tallafa musu ke raguwa.

Sakamakon shine: Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta bayyana cewar, iya kokarin da za ta iya yi shine, za ta iya tara kudin da za su isa ta tallafawa kaso 60 cikin 100 na mutane miliyan 307 da ta yi hasashe za su bukaci agaji a shekara mai kamawa. Hakan na nufin cewa akalla mutane miliyan 117 za su rasa abinci da sauran kayan agaji a 2025.

Za’a kare shekarar 2024 MDD ta iya tara kimanin kaso 46 cikin 100 na dala bilyan 49.6 da ta nema a fadin duniya a matsayin agaji, kamar yadda alkalumanta suka bayyana. Wannan ita ce shekara ta 2 a jere da MDD ke tara kasa da rabin kudaden da ta nema.

Gibin kudaden ya tilastawa hukumomin bada agaji daukar tsauraran matakai, irinsu zabtare yawan abinci da ake baiwa mutanen da ke fama da yunwa tare da rage yawan wadanda suka cancanci samun agajin.

Ana jin tasirin wadannan tsauraran matakai a wurare irinsu Syria, inda hukumar abinci ta duniya (WFP), babbar gabar MDD dake kula da rabon abinci, ke iya ciyar da mutane miliyan 6. Bayan nazarin hasashenta a kan gudunmawar kudaden agaji a farkon shekarar da muke ciki, WFP ta zabtare yawan mutanen da take burin taimakawa zuwa mutum miliyan 1, a cewar Rania Dagash-Kamara, mataimakiyar babban daraktan hukumar a kan kawance da tattara kudade.

Dagash-Kamara ta kaiwa ma’aikatan WFP da ke syria ziyara a watan Maris din daya gabata. “Umarnin da aka basu shine, “a wannan gaba muna karbewa ne daga masu fama da yunwa mu baiwa masu fama da matsananciyar yunwa.,” kamar yadda tace a wata zantawa da aka yi da ita.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG