Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an MDD Sun Tattauna Kan Makomar Dubban 'Yan Gudun Hijira A Nijar


Jami'an MDD lokacin wani taro a Nijar
Jami'an MDD lokacin wani taro a Nijar

Wasu manyan jami’an hukumar Majalisar Dinkin Duniya sun kammala ziyarar kwanaki da suka kai a Nijar, don tattauna batutuwan tsaro, yanayin bakin haure da ‘yan gudun hijira a jihar Agadez

Ziyarar ta ta’allaka ne kan tantance halin da ‘yan gudun hijira da bakin haure ke ciki a Nijar, musanman a jihar Agadez ind​a dubban bakin haure da ‘yan gudun hijira na kasashen Afirka ke zaune cikin yanayi na rashin tabbas game da makomarsu.

Taron MDD da wasu jami'ai a Nijar
Taron MDD da wasu jami'ai a Nijar

Tawagar, karkashin jagorancin Mohamed Abdiker, sun gana da hukumomin jihar Agadas inda suka tattauna batun da ya shafi tsaro, da kuma baiwa wasu ‘yan gudun hijira mafaka a kasar, da kuma batun sha’anin tafiyadda al’amuran bakin haure a jihar, da kuma inganta rayuwar talakawa inda hukumomin suka kafa wani sabon kwamitin da zai yi aikin tantance wadanda ya kamata a baiwa matsayin ‘yan gudun hijira daga cikin bakin.

Wani taron MDD a Nijar
Wani taron MDD a Nijar

Yanzu haka dai akwai kusan bakin haure sama da dubu dari dake jibge a sansanoni daban-daban dake cikin jihar Agadas yayin da ‘yan gudun hijira sama da dubu biyu da suka fito daga kasashen Libiya, Sudan da kuma Aljeriya.

Lamarin da yasa ‘yan Nijar suka sanar da tawagar matsayar su na su kwashe bakin hauren dake jibge da kuma rufe dukkanin sansanoni na karbar su dake cikin jihar baki daya.

Lokacin taron MDD a Nijar
Lokacin taron MDD a Nijar

A karshen ziyarar jami’an sun bayyana cewa hukumomin ba za su gaji ba wajen tallafawa ‘yan gudun hijira, sannan suka bayyana damuwa game dahalin da ake ciki a Sudan, wani lamarin da suka ce dole ne kasashen duniya su hada karfi don magance wannan matsala.

-Hamid Mahmud

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG