Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tace Rabin Al’ummar Sudan Na Tsananin Bukatar Agaji


Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

Majalisar Dinkin Duniya tace, sama da mutane miliyan 25, rabin al’ummar Sudan na bukatar agaji, sakamakon yadda fari ya mamaye wani yanki, yayinda mutane sama da miliyan 11 suka arce daga gidajen su.

Jakadan Amurka na musamman a Sudan a karon farko ya kai ziyara a kasar Sudan dake nahiyar Afrika a jiya litinin don neman karin tallafin jinkai ga miliyoyin mutanen da ke bukata da kuma kawo karshen mummunan yakin da ake gwabzawa.

Tom Perriello, wanda aka nada a matsayin jakadan Amurka na musamman a Sudan a watan Fabrairu, ya kai ziyara garin Port Sudan da ke gabar tekun Bahar Maliya, inda shelkwatar gwamnatin rundunar sojan kasar ta ke.

Wannan dai ita ce ziyarar farko da wani babban jami'in Amurka ya kai kasar tun bayan barkewar yakin da ake gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun RSF a watan Afrilun shekarar 2023, kuma an kwashe jami’an ofishin jakadancin Amurka daga babban birnin kasar.

‘’Muna cikin tsananin shaukin kawo karshen yakin nan, da kuma tabbatar da ganin faruwar hakan. Taimakawa da samar da abinci da magani da tallafawa rayuwar mutane miliyan 20 da doriya da ke cikin bukata’’ abinda wani jami’in ma’aikatar cikin gida ya fada kenan, kafin ziyarar.

Majalisar Dinkin Duniya tace, sama da mutane miliyan 25, rabin al’ummar Sudan na bukatar agaji, sakamakon yadda fari ya mamaye wani yanki, yayin da mutane sama da miliyan 11 suka arce daga gidajen su.

Perriello ya gana da shugaban sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan, da shugabannin hukumomin jinkai, da na gwamnati da shugabannin kabilu, a cewar wata sanarwa da ta fito da gakwamitin majalisar kasar.

A yayin wani taro kwamitin yace shugabannin biyu sunyi tattaunawa mai tsawo kan hanyoyin da za’a bi wajen shigar da agajin jinkai, da kuma samar da wata hanyar siyasa wajen kawo karshen yakin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG