Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Jigilar Maniyatan Najeriya Zuwa Kasa Mai Tsarki


Hajjin Bana
Hajjin Bana

A ranar litinin dan nan ne jirgin karshe dauke da ragowar alhazan Najeriya da sauran jami’an hukumar alhazai ya taso daga Birnin tarayya Abuja inda ya sauka a Birnin Madina, duk da cewa wasu daga cikin maniyatan rai yayi halinsa gabanin fara aikin hajjin na bana.

Jirgin karshen da ya sauka a filin tashi da jiragen sama na Yarima Bin Abdulaziz dake madina dauke da ragowar alhazai daga jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Bauchi, Abuja da kuma jihar Neja, jimilla su 211, ana kuma sa ran kamfanoni masu zaman kansu zasu kammala kwashe maniyatan su kafin rufe filayen jirgin sama na saudiyya.

Hajj
Hajj

A wata sanarwa da ta fito daga hannun jami’ar yada labaran hukumar NAHCON Hajiya Fatima Sanda Usara ta bayyana cewa a ranar 22 ga wannan watan bayan kammala aikin hajji hukumar zata fara dawo da alhazan Najeriya.

Shugaban ofishin kula da harkokin alhazai dake Madina, Alhaji Ibrahim Idris Mahmud, ya ja hankalin maniyata game da bin dokokin kasar Saudiyya inda ya jaddada muhimmancin katin sheda na maniyata da kasar Saudiyya ta fito dashi domin dakile masu kutse cikin alhazai.

Shugaban Ofishin Kula da Harkokin Alhazai dake Madina, Alhaji Ibrahim Idris Mahmud
Shugaban Ofishin Kula da Harkokin Alhazai dake Madina, Alhaji Ibrahim Idris Mahmud

Ya kuma bayyana cewa hukumar Saudiyya ta sanar dasu cewa duk wanda aka kamashi bada kati ko shaidar gudanar da aikin hajji ba, hukuncin shine biyan tara Riyal 10,000 tare da mai dashi kasar sa kuma sai bayan shekara 10 kafin ya kara shiga kasar Saudiyya.

Game da lafiyar alhazai kuma tawagar likitocin Najeriya ta sha damarar wayar da kan alhazai kan daukar matakan kaucewa zafin rana daka iya haifar da matsalar matsanancin zafi ko 'heat stroke' a turance da ka iya barazana ga rayuwar su da kuma jaddada muhimmancin shan ruwa inji jagoran tawagar likitocin dake kula da alhazan Dr. Abubakar Adamu Ismail.

Hajji Bana
Hajji Bana

Shugaban Izala (JIBWIS) na Najeriya Sheik Abdullahi Bala Lau ya bawa alhazan shawar ne dasu gudanar da aiyukan su na ibada kamar yadda addinin Islama ya karantar.

Duk da cewa wannan shine ya zama mafi tsadar kujerar hajji a tarihi wasu daga cikin alhazan sun bayyana ra’ayinsu da samun wannan dama, inda suka yaba da dukkan ayyuka da tsare-tsare na hajjin bana.

Saurari rahoton Hauwa Umar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG