Lauyar rundunar ‘yan sanda Barista Muleng Alex ta karanta wa wadanda ake zargin laifukansu da suka hada da yin amfani da wukake da adduna da takobi wajen kisan mutanen, ta kuma ce idan har aka same su da laifi, hukuncinsu shine kisa.
Sai dai wadanda ake zargin sun musanata zargin da ake musu.
Lauyan dake kare wadanda ake zargin, Barista Yakubu Sale Bawa ya bukaci a baiwa kowannensu kofi na zargin da ake mishi maimakon kofi daya da aka basu gaba daya.
Alkalin kotun, Mai shari’a Arum Ashoms, ya ba da umurni a tusa keyar wadanda ake zargin zuwa gidan gyara hali har sai ranar 13 ga watan Oktoban 2021 don fara sauraren shaidu.
Yayin da daya daga cikinsu, Solomon Dung mai shekaru goma sha bakwai aka tura keyarsa zuwa gidan gyara hali na yaran da basu kai shekaru goma sha takwas ba.
A tsakiyar watan Agusta aka tare matafiyan wadanda suka ratsa ta birnin Jos domin kai wa ga jihar Ondo aka kashe mutum sama da 20 a cikinsu.
Sun fito ne daga wani taron addini a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya a jerin wasu motocin bas-bas.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.