Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Ya Kai Ziyara Jihar Filato


Laftanar Janar Faruk Yahaya (Facebook/Nigerian Army)
Laftanar Janar Faruk Yahaya (Facebook/Nigerian Army)

Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ce sojin Najeriyar za su ci gaba da aiki tare da gwamnatin Jihar Filato don maido da zaman lafiya da tsaro a cikin jihar.

Babban hafsan, wanda ya zo ziyarar aiki a garin Jos, ya kuma ce rundunar da ke samar da tsaro a Jihar Filato ta Operation Safe Haven da runduna ta uku dake Jos, zasu ci gaba da aikin kakkabe bata gari dake haddasa rashin zaman lafiya a jihar.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya yaba ne da kokarin jami’an sojin wajen yaki da ‘yan ta’adda a sassa daban daban na kasar.

Komishinan yada labarai da sadarwa a Jihar Filato, Dan Manjang ya ce ziyarar ta hafsan sojin na da muhimmanci sosai ga zaman lafiya a cikin Jihar Filato.

Sauari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Ya Kai Ziyara Jihar Filato
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG