Madam Kube Maxwell daya daga cikin matan 'yansandan da suka rasa mazajensu lokacin da aka kaiwa 'yansandan hari a garin Gamboru-Ngala ranar biyar ga watan Mayun wannan shekarar, tayi jawabi lokacin da matan ke karbar taimakon kudi nera guda guda daga gwamnatin jihar Borno. Kowace mace da ta rasa mijinta ta samu nera miliyan daya. Matan wadan da mazansu sun samu rauni su ma an masu nera dari biyu. Mata goma sha shida suka rasa mazansu.
Harin da aka kai akan garin Gamboru-Ngala yayi sanadiyar asarar rayuka masu yawa da dimbin dukiyoyi. Madam Maxwell tace ba abu mai sauki ba ne ace mijinki ya fita aiki amma bai dawo ba sai kawai a kawowa mutum gawarsa.Tace abu ne mai matukar tayarda hankali. Sabili da haka ta roki gwamnati ta samarma sauran mazajensu makaman aiki domin kare kansu da kuma jama'a baki daya. Ta kuma roki hukumar 'yansandan da ta hanzarta fitar masu da hakkokin mazajensu domin rage masu irin halin wuyan da suka fada ciki yanzu.
Daya daga cikin 'yansandan da suka samu rauni yace abun da suka gani abun alajabi ne. Yace sun gode da taimakon gwamnati amma ba bukatarsu ba ne a dinga taimaka masu kodayaushe suka ji rauni. Bukatarsu ita ce a samu zaman lafiya kuma gwamnati ta duba domin su har yanzu basu gane abun dake faruwa ba. Yace yaya za'a ce ana fada a kira sojoji ba zasu zo ba. Su suna Gamboru sojoji kuma suna Ngala amma suka ki su kawo masu dauki.
Abdullahi Dogara daga Lafiya jihar Nasarawa daya daga cikin wadanda suka rasa 'yanuwa yace ya gode da tallafin da gwamnatin Borno ta yiwa danuwansa Muhammed Salihu. Alhaji Lawal Tanko kwamishanan 'yansandan jihar Borno yace gwamnatin jihar Borno ta bayar da kudi domin a tallafawa iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka ji ciwo.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.