Idan ba'aanta ba ita kungiyar Boko Haram tana ikirarin yin abubuwan da ta keyi domin yin jihadi da kuma kaddamar da mulkin Islama a kasar. Wannan ikirari nasu wata hanaya ce ta shafawa addinin Islama kashin kaza. Sabili da haka kungiyoyin musulunci sun shiga wani halin damuwa.
Dr Khalil Abubakar sakataren kungiyar Jama'atul Nasril Islam ko JNI a takaice yace akwai kalubale na yadda za'a kawar da bakin fentin da ake so a shafawa addinin Musulunci. Wadanda suke so su bata Muslunci suna iya fakewa da abubuwan da Boko Haram keyi. Misali, yace kafofin yada labarai suna anfani da kalmomi masu rauni, kamar kiran 'yan Boko Haram "mutane masu kishin Islama". Suna bukatar 'yan jarida da su daina anfani da kalmomi makamantan hakan.
Shi ma shugaban kungiyar Izala a Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau yace tabbas akwai kalubale a gabansu. Yanzu musulmai suna cikin wani halin abun tausayi. Sabili da haka dole ne shugabannin addinin su tashi su karantar da al'umma kyawawan dabi'u da halaye na addinin Musulunci domin ana neman a shafawa addinin kashin kaza.
Yayin da kungiyar Boko Haram ta kunno kai wasu malamai sun sha kai da kawowa suna fadakar da kawunan mutane. Sheikh Abubakar Giro Argungu yana daga cikin wadadan nan malaman. Ya share sama da shekara uku zuwa biyar yana koyaswa da yin anfani da gidajen telebijan da na radiyo a jihohin arewa maso gabas da ma wasu wuraren yana bayyana munin kirkiro irin akidar Boko Haram.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.