Mr James Abawus Watarda shugaban karamar hukumar Madagali yace lallai suna fuskantar mawuyacin hali a garin. Na daya basu da tsaro ko kadan. Na biyu suna iyaka ne da jihar Borno. Duk abubuwan dake faruwa a Borno yanzu sun karkato zuwa Adamawa musamman a nasu yankin na Madagali. Karamar hukumar Madagali ita ce tafi kusa da jihar Borno kuma tana gaf da dajin Sambisa inda 'yan Boko Haram suka ja daga. 'Yan bindiga na iya takawa da kafa daga dajin su shiga Madagali.
Shugaban yace karamar hukumarsu bata da wani karfi yadda zata iya ta dauki wani mataki na kare kanta. Abu daya zasu iya yi shi ne idan mutanensu sun gudo daga wani wuri sai su basu wurin zama. Amma batun tsaro hakkin gwamnatin tarayya ne. Ko gwamnatin jiha bata da karfin tanada tsaro. A halin da suke ciki kowane sati ana kai masu hari.
Mazauna garin basu da komi fiye da kwari da baka ko adduna. Wadannan kuma basu da anfani domin yanzu bindigogi ake anfani dasu. Babu abun da zasu iya yi saidai su gudu idan an kawo masu hari. Ya karkare da rokan gwamnati ta taimaka da jami'an tsaro.
Ga firar.