Fadar White House ta shugaban Amurka tana maida murtani mai zafi akan matakin da alkalin wata kotun Amurka ya dauka na takawa sabon umurnin shugaba Donald Trump burki, wanda ya so ya hana baki daga kasashe da yawa shigowa Amurka daga yau Laraba.
“Mummunan matakin da kotun tarayya ta dauka yau ya lalata kokarin shugaban kasa na kare rayukan Amurkawa da kuma sanya dokokin da suka dace akan shigowa Amurka, a cewar sanarwar ta fadar White House da aka fidda jiya Talata, jim kadan bayan da alkali Derrick Watson ya yanke hukunci akan dakatar da dokar hana baki daga kasashe shida, da gwamnatin Trump ta ce sun gaza bada isassun bayanai da cika ka’idodin tsaro domin shiga Amurka.
Inda ba don matakin alkalin ba, da dokar ta hana matafiya daga kasashen Chadi, da Iran, da Libiya, da Somaliya, da Siriya da kuma Yemen shigowa Amurka daga yau Laraba.
Facebook Forum