Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Iraqi Sun Kwato Manyan Filayen Hakar Man Fetur daga Kurdawa


Dakarun Iraqi ke nan suna murnar nasarar da suka samu
Dakarun Iraqi ke nan suna murnar nasarar da suka samu

Sannu a hankali, dakarun Iraqi sun kutsa kai cikin arewacin kasar a ranar Talata, inda suka kwato ikon wasu yankuna hade da wasu manyan filayen hakar mai daga Kurdawa, lamarin da ake ganin ya kawo karshen burin Kurdawan na kafa kasarsu.

Kwana guda bayan karbe ikon Kirkuk, Birnin da ke da yawan jama’a miliyan guda, dakarun Bagadaza sun karbe ikon garuruwan da kewayensu, wanda hakan ya sa Kurdawa suka ja da baya ba tare da nuna wata turjiya ba.

Filayen hakar main a Bai Hasan da Avana, su suke samar da gangar mai kusan dubu 250 a kowace rana daga cikin dubu 650 na gangar mai da yankin Kurdawa mai cin gashin kansa yake fitarwa zuwa kasashen waje domin samun kudaden gudanar da ayyukansa.

Kuma wannan galaba da aka samu a kansu babban koma baya ne ga fannin tattalin arzikinsu na neman ballewa daga gwamnatin tarrayar Iraq.

A watan da ya gabata ne Kurdawan suka gudanar da zaben raba gardama domin kafa kasar, zaben da hukumomin Bagadaza suka ce haramtacce ne.

Amurka ta horar dakarun Iraqi da mayakan Kurdawan Peshmerga, inda ta kan hada kai da su domin yakar ISIS. Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Litinin ya ce Amurka ba ta bi bayan kowa ba yayin da ake kai ruwa rana kan shugabanci a arewacin Iraqi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG