Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata a Arewacin Nijeriya na Fuskantar Babban Cikas


Wasu mata a Nijeriya da ke cikin halin ni 'yasu
Wasu mata a Nijeriya da ke cikin halin ni 'yasu

An sake jaddada muhimmancin ilimi ga mata da yara saboda ko da wani abu ka faru da mai gida kamar mutuwa ko nakasa; ko kariyar sana’a ko kuma saki, mace mai ilimi ko ‘ya’ya masu ilimi na iya ciyar da kankasu.

Shugabar Gidauniyar Isa Wali mai kula da tsaro, lafiya da kuma ilimin mata da ke Kano mai kula da Hajiya Amina Wali Hanga, ta ace amma abin takaici ana jinkiri wajen ilimantar da ‘ya’ya mata. Ta ce shi ya sa ma addinin Musulunci ke ba da muhimmanci ga ilimin mata da yara. Ta ce baya ga batun ilimi ma, sun a duba batun lafiyar mata da yara.

Ta ce batun lafiyar mata masu cigaba abu ne mai muhimmancin. Don haka su na mai da hankali kan wannan ma sosai. Ta ce baya ga haka ma sun a ba da himma wajen tabbatat da ‘yancin mata ta wajen bin hanyar da ta dace saboda kauce ma cin karo da tanaje-tanajen addini da ala’ada.

Da ta sake juyowa ga batun ilimi, sai ta ce yanzu haka kididdiga daga makarantun gaba da firamare na nuna cewa mata, wadanda ke kammala makarantar sakandare ba su wace kashi 4% zuwa 5% ba. Haka kuma masu kammala Jami’a ba su wuce kashi 2%.

##caption:Wasu mata a Nijeriya da ke cikin halin ni 'yasu.##

XS
SM
MD
LG