Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji da Zaben Najeriya


Air Marshal Alex Badeh
Air Marshal Alex Badeh

Matasan Nijeriya na cigaba da bayya ra’ayoyinsu game da rawar da sojoji ke takawa a zaben Nijeriya. A yayin da wasu ke ganin ya kamata sojoji su taka rawa, wasu kuwa gani suke bai kamata su taka wata rawaba saboda ba aikinsu Kenan ba. Mai Magana na farko yace ko a tsarin mulkin Nijeriya, ‘yan sanda da masu tabbatar da tsaro na farin kaya ne ya kamata su yi aikin tabbatar da tsaro a lokutan zabe amma ba sojoji ba musamman dayake yanzu lokaci ne na dimokaradiyya.

To saidai kuma mai magana na biyu y ace a halin da ake ciki na tabarbarewar tsaro, ya kamata sojoji su yi dumudumu a harkar zaben Nijeriya. Y ace ta haka ne kadai za a iya kare akwatunan zabe da kuma lafiyar jama’a da dukiyoyi daga miyagu. Shi kuwa mutum na biye cewa ya yi ganin soja kawai ma na iya tsorata masu kada kuri’a. Wakiyarmu wadda ta aiko da wannan rahoton, Baraka Bashir ta yi nuni da yadda Kotun Daukaka Kare ta Abuja ta ce amfani da soji a wurin zabe ya saba ma kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Baraka ta yi nuni da yadda ake ta samun sa’insa tsakanin jam’iyyu game da hukuncin kotun. Anan sai Dandalin VOA ya tuntubi Prof Muhammad Habu Fagge na Jami’ar Ado Bayero ta Kano, ya ce batun tura soja wuraren zabe aiki ne na kasashen da bas u cigaba ba. Ya ce kwanan nan aka gano cewa an yi amfani da sojoji wajen tabka magudi. Don haka shi ya na ganin muddun ba al’amura ne su ka lalace sosai ba, to bai kamata a saka soji cikin harkokin zabe ba.

##caption:Air Marshal Alex Badeh.##

XS
SM
MD
LG