Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanyoyin da Malamai ke Samun Kudaden Shiga


Wata hanya da malaman jami’o’I, masana da marubuta kan samu karin kudin shiga, baya ga albashin su a nan kasar Amurka, itace, su kan buga littatafai da kuma sai dasu da tsada.

Al’umah naganin cewa wannan wani koma baya ne ga tattalin arzikin kasa. Kasancewar dalibai na gama karatun jami’o’i, da dinbin bashi a kansu.

A ganin wasu ‘yan majalisu daga karamar hukumar Pallyup a jihar Washington a Amurka, na ganin yakamata asa adadin kudi da marubucin littafi zai iya sayarda littafin shi.

A ganin dan majalisa, Hanz Zeiger, yana ganin kowane marubuci kada ya wuce sayarda littafinshi samada dalla Amurka $100 kwatankwacin Naira 21,000 kudin Najeriya. Shi kuwa dan majalisa, Melanie Stambaugh, yana ganin kamata yayi a fito da wani tsari wanda malamai zasu gudanar da koyarwa ta hanyar bidiyo wanda dalibai zasu iya gani a shafufukan yanar gizo.

Duk dai suna kallon wannan abun wata hanya ce ta samun makudan kudi ga marubuta.

XS
SM
MD
LG