Nan bada dadewa ba gwamnatin tarayya Nigeria zata mayar da sai kana da shedar samu digiri kafin ka fara koyarwa a kowacce makaranta kasar.
Ministan illimi na Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau ne ya furta haka a lokacin da jakadan kasar Finland Pirjo Suomel-Chowdhury ya kai masa ziyara ofishin sa.
Minista Shekarau yana maida martini ne ga bayanin da jakadan kasar Finland ya yi cewa, a kasar sa duk Malaman makaranta, sai suna da digiri kafin ma a dauke su aikin koyarwa, domin aiki ne da ake gasar samun sa, domin akwai kwararun mutane da yawa dake neman aikin.
Shekarau dai ya lura cewar gwamnatin tarayya za ta yi duk abinda ya kamata domin maido da mutunci, da kuma daraja malamai a kasar. Ya kuma kara jaddada cewa burin gwamnatin tarayya shine maida shedar samun digiri a zaman mafi kankanci kwarewar zama malamin kowacce makaranta a kasar. Ya kuma ce tun shekara ta alif 1980, shedar da ake bukata ga malamin makaranta shine shedar gama kwalejin horas da malamai na gaba da sakandare da ake cewa NCE.
Ya bayar da tabbacin cewa, sannu kan hankali wannan zai canza, domin za’a mayar da shi ya zamanto sai kana da shedar samun digiri, har ma yace akwai masu digiri dake koyarwa a makarantun firamare a yanzu haka a kasar.
Ya kara da cewa sannu a hankali za’a kai ga inda aka nufa. Tare da fatan wata rana zai zamanto masu digiri ne ke koyarda da duk makarantun Nigeria.