Shugabannin addini dana al'umma sun gargadi ‘yan siyasa da kuma yan korensu dasu ‘kauracewa irin maganganun da zai kawo matsala a tsakanin mabiya da kuma cusa kiyayya a tsakanin jinsuna.
Shugabannin sunyi wannan gargadine a taron zaman lafiya tsakanin musulmi dakuma kirista da aka gudanar a majami'ar ecwa a garin bauchi.
Mallam Usaman Shagari Adamu, shine ya jagoranci al’ummar musulmi a taron, inda yace, “Babban makasudin tara jama’a a nan gurin cikin wannan haraba ta majami’ar dake Bauchi, shine bisa ga iko na ubangiji mun fara samo inda bakin zarenmu ya tsinke, kuma mun fara kokarin dinkeshi, tunda ka ganmu cikin coci mun taru don mu hada kai a kan wannan al’amari.”
Rabaran Dakta Shu’aibu Gayil, shine mai masaukin da aka gudanar da taron a mijami’ar sa inda yace, “manufar mu shine yunkurin son zama lafiya, babban abin kalubale garemu shine bamu damu da abin wani keyi a can ba, a kwai bukatar wanda ke can yana yin abinda ya ga dama, sai muja masa hankali ta wajen hadin kanmu, domin in yazo bazai same mu a rarrabe ba.”
Shi kuma Alhaji Garba Muhammad Noma Jarman Bauchi, yayi tsokacine kan irin maganganun da wasu ke shiga kafofin wasa labarai suna bayyanawa, inda yace hakan bazai taimakawa zaman lafiya ba, ya dai ce a kwai wasu abubuwa da suke faruwa a kasar nan inda yake ganin ba zasu zama abin alkhairi ga kasar nan ba, saboda wasu na amfani da kafofin wasa labarai na gwamnatin tarayya da makamantansu, suna fadin abubuwan da zai zama abin cutarwane ga kasar baki daya. Musammam Arewa ana son a hada mu fada na addini dana kabilanci.
##caption:Musulmi da Kristoci. (File Photo)##