Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed, ne yayi wannan sharhin na illolin yaki bayan da ya dawo daga ziyara a yankunan da sojoji suka kwato daga hannun ‘yan boko haram da aka fatattaka yanzu haka, ya kuma yi hanunka mai sanda akan yadda yaki kan daidaita al’umma.
Tun bayan kama kakakin masu rajin kafa Biafra, Nnamdi Kanu mai yada kiyayya a gidan rediyonsa mara lasisi, magoya bayan wannan akidar ke tada kura a yankin. Ko me jami’an gwamnati ke yi don kwantar da wannan kurar? Tambayar da wakilin sashen Hausa Nasiru Adamu El-hikaya ya yi wa ministan matasa da wasanni barista Solomon Dalung Kenan.
Ministan na matasa ya ce gwamnati za ta yi dirar mikiya akan masu zuga matasan don kawo karshen matsalar. Ya kara da cewa wasu ne ke tunzura matasan amma su suna gefe guda. Daukar mataki akan masu daukar nauyin matasan da tunzura su shi hukuma zata yi, saboda ba ra’ayin su ne..
A nata bangaren, jam’iyyar adawa ta PDP na ganin akwai bukatar shugaban kasa Mohammadu Buhari ya yi zama da matasan don shawo kansu a cewar sakataren labaran PDP Olisa Metu. Sakataren ya karfafa wannan bukatar akan cewa an kai matasan bango ne wajen nuna wa yankinsu wariya, shi ya su daukar wannan matakin.
Barrister Solomon Dalung kuma ya shawarci matasan arewacin Najeriya akan kada su nemi tada fitina akan dalilin ana nuna wa ‘yan arewa dake yankin kudu maso gabashin Najeriya kiyayya.
Ga karin bayani.