A cigaba da yaki da barayin shanu a Najeriya rundunar 'yansandan kasar reshen jihar Neja ta samu cafke wasu barayin su 24 tare da kwato shanu 433 a hannunsu.
A wani taron manema labarai kakakin 'yansandan ASP Bala Elkana yace a halin yanzu suna samun nasara da yaki da barayin shanun a karkashin wani shiri na musamman. Sun yi shirin ne domin yaki da matsalar a jihar ta Neja.
Banda samun kama barayin su 24 'yanasandan sun kashe guda kana suka kwato miyagun makamai guda shida.
Yanzu dai 'yansandan sun kai mutanen kotu, saura kuma ya rage ga alkalin da zasu fuskanta.
Akan yadda suke samun barayin ASP Elkana yace sabon kwamishanansu Abubakar Marafa ya baza jam'an leken asiri ya yi suna bin sawun barayin shanu a duk fadin jihar. Ta dalilin haka 'yansandan sun gano dazuka bakwai da barayin ke samun mafaka.
An soma mika shanun satan ga masu su. Wani Abdullahi Ardo yace ya ji sanarwar da aka bayar a radiyo dalilin zuwansa ke nan kuma ya samu shanu 27 daga cikn nasa da aka sata. Wani Shaiabu Jere daga jihar Kaduna yace shi ya ga daya daga cikin nashi 36 da aka sace.
Ga karin bayani.