Lauyoyi da ‘yan jarida, ‘yan siyasa da ma’abuta kafofin sada zumunta na zamani na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da kudirin dokar takaita amfani da kafofin sada zuminci na zamani dake gaban majalisar dattawan Najeriya.
Wannan kudirin doka da Sanata Bala Ibn NaAllah daga jihar Kebbi ya gabatar da yanzu haka ya tsallake karatu na biyu a azure majalisar dattawan ta Najeriya, ya tanaji dauri shekaru biyu a kurkuku ko tarar Naira miliyan biyu ga duk mutumin da aka samu da laifin batanci ko cin zarafi ga wani ko wasu a shafukan sada zumunci na zamani.
Murtala Saleh Tambari, wani dan jam’iyyar APC, a kano, ya ce shugabani ‘yan majalisa ko zababbu suna so suyi wannan abun ne akan kansu baiwai akan abunda ya shafi al’uman kasa da kuma abunda ya shafi kasar mu ba da hadin kan kasarmu ba, ace za’a yi wata doka wace yanzu ai’umar wanna kasa suka zo ga wanna ci gaba da ya samu duniya ta harkar waya maganan social media, toh dayawa za’a kama fiye da rabin al’umar kasan nan a kule.
Malam Ali Sanusi, daya daga cikin miliyoyin ‘yan Najeriya, dake hulda da kafofin sada zumunta na zamani a kowace rana cewa yayi an ci moriyar ganga za’a yada kwaurenta domin abaya jam’iyyar APC, dake da Gwamnati yanzu tayi amfani da kafofin sada zumunci wajen yada furofaganda da manufufinta .
Tuni dai Masana dokoki da sharia ke fasara lamarin a matsayin wani salon hawan kawara ga dokokin Najeriya, dama dokokin kasa da kasa da Najeriyar ta rattabawa hannu game da yancin bil-Adama ta fuskar furta ra’ayi ko bayanai.