Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-zanga A Bingi Sun Datse Hanyar Sokoto Zuwa Zamfara


Masu zanga zanga a Bingi
Masu zanga zanga a Bingi

Al'umar Bingi cikin Karamar Hukumar Bungudu, a Jihar Zamfara dake arewacin Najeriya, sun datse hanyar Sokoto zuwa Zamfara don neman dauki daga gwamnati dangane da karuwar harin 'yan Bindiga a yankinsu.

Da misalin karfe goma na safiyar jiya ne maharan suka kai hari a kauyukan Juyi da Dorayai a karkashin garin Bingi, suka harbi mutane 6, suka sace mata sama da 20 suka gudu daji.

Mazaunin yankin Mallam Kabiru, ya bayyana wa wakilin Muryar Amurka cewa, barayin sun samu labarincewa an kai sojoji kasuwa Bingi mai chi duk mako, shi yasa suka juya zuwa kauyuka Juyi da Dorayai. Daga nan sun ci gaba da yi barin wuta in da suka kashe mutane da dama.

Kabiru ya ce, sun kai ruhoto ga jami'an tsaron dake yankin amma sunce ba a basu umarni ba. Hakkan ne ya fusatar da jama’ar kauyukan yanki suka tare hanya, maza da mata da yara suna kona tayoyin mota a kan titi.

Mai Martaba Sarkin Anka ya ce shi da kansa ya lallashe su amma sun ki saboda lamarin ya kai su makura domin harbi sama da sojoji suka yi bai razana matan ba balle kuma maza.

Wani Matafiyi ma yace sun jima a hanyar ba mafita. Ya ce an zo wuce da mara lafiya daga asibin Gusau zuwa sokoto, sai suka ki a bude hanya domin ran su ya baci. Hatta matafiya da a kafa ana hanu su wucewa.

Daga bisa ni Kakakin Rundunar Yan Sanda ta Jihar Zamfara, SP Shehu Muhammad ya bayyana cewa yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar, aka bude hanya matafiya suka wuce.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG