ABUJA, NIGERIA - A rumfuna da dama da wakilanmu suka zagaya a Abuja babban birnin Najeriya, sun ga masu zabe kan layi suna kada kuria’r su ba tare da wani cikas ba.
Wakilan jam’iyyu na sanya ido kan zaben da nuna kyakkyawar fata cewa za'a kammala zaben lafiya kuma gwanayen su za su sami nasara.
Wani abin da ya dauki hankali shi ne sabbin rumfunan zabe da a ka kirkiro inda a wata rumfa a anguwar AREA 3 a Abuja a ke da masu zabe 6 kacal, alhali akwai jami’ai kusan 7 da ke kula da rumfar.
Hajiya Saudat Abdullahi da ta kada kuri’a, ta yi zargin an so nuna ma ta wariya ta fuskar kabilanci, amma taimakon wasu matan majami’a ya sa ta sami nasarar yin zaben.
Abun da ya fi fitowa fili shi ne yanda masu kada kuri’a ke fatan ko dai Allah ya ba mai rabo sa’a, ko kuma sa’ar ta zama ta su.
Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu da zai bude dakin tattarawa da bayyana sakamakon zabe ya nuna kwarin gwiwar komai ya na tafiya bisa yadda a ka tsara.
Da alamu dai zabe ya kammala ko ya na daf da kammala inda za'a soma jiran sakamako ya zama na kai tsaye; a samu wanda ya lashe ko a iya zuwa zagaye na biyu.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya: