Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Damokaradiyar Najeriya Tana Da Tasiri A Kasashen Duniya- Mark Green


Ambasada Mark Green, Shugaba kuma Babban Jami’in Cibiyar Nazarin Kasa da Kasa ta Woodrow Wilson,
Ambasada Mark Green, Shugaba kuma Babban Jami’in Cibiyar Nazarin Kasa da Kasa ta Woodrow Wilson,

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana kamala shirye shiryen babban zabe na kasa da za a fara gobe da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarraya, zaben da tuni daruruwan masu sa ido daga kasashe da kungiyoyi dabam dabam na duniya suka isa kasar domin ganin yadda zai gudana.

A hirar shi da Muryar Amurka, Ambasada Mark Green, Shugaba kuma Babban Jami’in Cibiyar Nazarin Kasa da Kasa ta Woodrow Wilson, daya daga cikin tawagar masu sa ido kan zaben daga Amurka ya bayyana muhimmancin zaben Najeriya.

Ya ce, " Wannnan ne aikin sa ido a zabe da ya kunshi mutane masu sa ido da yawa, kuma na sha zuwa sa ido a zabuka a kasashen duniya da dama, amma babu inda mu ka yi yawa haka. Ina jin ya nuna muhimancin Najeriya da kuma muhimmancin damokaradiya a Najeriya.

Aikinmu mu shi ne sa ido a kan yadda ake gudanar da zabe mu kuma zama ido a ci gaban da Najeriya ta samu a fannin damokaradiya. Mu ba sahabai ba ne. ba mu ce mun iya ba. A fili ya ke cewa, Najeriya ta dauki lokaci ainun ta kuma zuba jari wajen ganin ci gaban damokaradiya, abinda mu ka zo mu gani ke nan."

Dangane da binciken da Cibiyoyin su ka gudanar na hadin guiwa kan harkokin damokaradiya a Najeriya Jakade Mark Green ya bayyana cewa,

Kungiyoyi biyu sun gudanar da bincike musamman kan abinda ya shafi ‘yan gudun hijira na cikin gida watanni da suka gabata, aka kuma ba hukumar zabe shawarwari, wadanda hukumar ta riga ta aiwatar da wadansu daga ciki, haka zamu yi yanzu ma, za mu zuba ido mu gani da farko, kamar yadda na fada , Najeriya ta na kan hanya ne kamar sauran kasashe na duniya, saboda haka zamu sa ido daga baya kuma mu bada shawarwari da hukumar zabe, da kuma kasar zasu iya amfani da su.

Ambasada Mark Green, Shugaba kuma Babban Jami’in Cibiyar Nazarin Kasa da Kasa ta Woodrow Wilson,
Ambasada Mark Green, Shugaba kuma Babban Jami’in Cibiyar Nazarin Kasa da Kasa ta Woodrow Wilson,

Da aka tambaye shi ko yana gani wannan sake fasalin takardun kudin da aka yi a daidai lokacin zabe zai shawo kan matsalar sayen kuri’u da binciken cibiyoyin ya ambata a rahoton da ya fitar sai ya bayyana cewa,

"A matsayinmu na masu sa ido, hakinmu shi ne sa ido ba zamu yi shaci fadi ba. Lamari ne mai sarkakiya. Ko wannan zai yi tasiri? Abu ne da za mu jira mu gani. Najeriya wata kasa ce mai rikitarwa, kasar da ta ke da harsuna dabam dabam guda dari biyar da kabilu da kuma al’adu dabam dabam, sabili da haka, kasa ce mai rikitarwa, daya daga cikin abinda za mu yi shi ne mu hada hannu da hukumar zabe da kuma hukumomi wajen karfafa damokaradiyar kasar."

Dangane da ko hukumomi sun aiwatar da shawarwari 23 da cibiyoyin su ka bayar a rahotonsu, da su ka shafi zabe sai Jakade Green ya bayyana cewa,

An aiwatar da wadansu, shawarwarin da muka bayar dangane da wadanda su ka kauracewa matsugunansu wadansu an aiwatar, kasancewa abu ne da za a bi mataki mataki. Na sani hukumar zabe tana namijin kokari. Dukanmu burinmu daya ne. Mun ji dadin cewa, an karbi shawarwarin da mu ka bayar da hannu biyu ana kuma nazarinsu, zamu sa ido tare domin ganin ci gaban da za a samu.

iri.org/resources/statement-of-the-second-joint-ndi-iri-pre-election-assessment-mission-to-nigeria/

Dangane kuma da shirin da hukumar zabe da jam’iyun siyasa da kuma daidaikun jama’a su ka yi na wannan zaben sai jakade Mark Green yace

Zan iya cewa, daga abinda na ji na kuma gani tun lokacin da na shigo kasar kwanaki da su ka shige, da kuma irin rawar da na ga kungiyoyin fararen kaya su ke takawa, abin ya burge ni ainun. Ina jin akwai sauran aiki, sai dai kamar yadda na ce, Najeriya kasa ce mai sarkakiya mun sani za a bukaci yin aiki, sai dai na sani an yi aiki sosai. Abinda ya burge ni shine irin kishin kasan ‘yan Najeriya.

‘Yan Najeriya suna matukar farin cikin samun damar da za a saurare su. Sun yarda da kasarsu, sun yarda da damokaradiya. Wannan ne zabe na farko a nahiyar Afrika bana, amma ba shi ne zai zama na karshe ba. Akwai wadansu da za su biyo baya, sai dai wannan zabe ne na damokaradiya mafi girma a Afirka, a daya daga cikin jariran kasashe na duniya, sabili da haka idan aka hada wadannan duka, ba abu ne da ya shafi Najeriya kadai ba, abu ne da ya shafi duniya baki daya. Saboda haka, wannan yana da muhimmanci ga Najeriya, yana da muhimmanci ga matasan Najeriya, yana da muhimmanci ga duniya baki daya. An yi Imani da cewa, gudanar da zabe mai sahihanci a nan, da kuma nasarar damokaradiya, ba kimar Najeriya kadai ya ke dagawa ba, amma, karfin damokaradiya a nahiyar da kuma duniya baki daya.

Banda wannan tawagar masu sa ido mai mutane 40 ta kungiyar hadin guiwar NDI da IRI da ta kunshi jami’an diplomasiya da manyan kusoshin gwamnatocin kasashe 20, kungiyar Tarrayar Turai ta tura kusan masu sa ido dari, banda masu sa ido na Kungiyar hadin kan kasashen Afrika da kuma wadanda wadansu kasashe da kungiyoyi masu zaman kansu suka tura wadanda zasu rarrabu a dukan jihohin Najeriya 36 domin ganin yadda za a gudanar da zabe da ake gani zai zama mai cike da tarihi, kasancewa shine na farko da aka sami ‘yan tsayayyun ‘yan takara daga wadansu jam’iyu da suka dauki hankali da samun gagarumin goyon baya, banda jam’iya mai mulki da kuma babbar jam’iyar adawa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG