Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Tarihin Peter Obi Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar Labour


Yakin neman zaben Peter Obi
Yakin neman zaben Peter Obi

Kafin ya shiga siyasa, Obi dan kasuwa ne wanda ya rike mukamai da dama a wasu masana’antu masu zaman kansu, ciki har da Next International Nigeria Ltd, da Guardian Express Bank Plc, da sauransu.

An haifi Mista Peter Obi ne a ranar 9 ga watan Yulin shekarar 1961 a garin Onitsha na jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Ilimi
Bayan ya kammala makarantar firamare, Obi ya halarci Christ the King College, inda ya kammala karantun sakandare. Daga nan ya samu shiga jami’ar Najeriya da ke garin Nsukka a shekarar 1980, inda ya samu digiri a ilmin Falsafa a shekarar 1984.

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi

Daga nan kuma Obi ya halarci Lagos Business School a birnin Legas na Najeriya, da Harvard Business School da ke birnin Massachusetts na Amurka, da London School of Economics a Ingila, da Columbia Business School, da kuma Institute for Management Development da ke kasar Switzerland. Bayan haka ya je kwalejin Kellogg Graduate School of Management a Amurka, da Said Business School da ke jami’ar Oxford a Ingila, da kuma Judge Business School ta jami’ar Cambridge a Ingila.

Sana'a

Kafin ya shiga siyasa, Obi dan kasuwa ne wanda ya rike mukamai da dama a wasu masana’antu masu zaman kansu, ciki har da Next International Nigeria Ltd, da Guardian Express Bank Plc, da Future View Securities Ltd, da Chams Nigeria Ltd, da Paymaster Nigeria Ltd, da kuma Fidelity Bank Plc.

Siyasa

A shekarar 2003, Obi ya shiga fagen siyasa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Anambra na jam’iyyar APGA, inda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar PDP Chris Ngige a matsayin wanda ya lashe zaben, amma a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2006, kotun daukaka kara ta ayyana Obi a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamnan.

Datti Baba-Ahmed, hagu, da Peter Obi, dama (Hoto: Facebook/Peter Obi Movement)
Datti Baba-Ahmed, hagu, da Peter Obi, dama (Hoto: Facebook/Peter Obi Movement)

An rantsar da Obi a matsayin gwamnan jihar Anambra a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2006. Majalisar dokoki ta jihar Anambra ta tsige Obi daga gwamna a ranar 2 ga watan Nuwamban shekarar 2006, inda mataimakiyarsa Virginia Etiaba ta maye gurbinsa a matsayin gwamna mace ta farko a tarihin Najeriya. Amma Obi ya kalubalanci tsige shi da majalisar jihar ta yi, kuma kotun daukaka kara ta dawo da shi kan kujerar gwamnan jihar Anambra a ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar 2007.

Obi ya sake barin kujerar gwamna a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, biyo bayan zaben da aka gudanar, wanda dan takaran jam’iyyar PDP Andy Uba ya lashe. Amma Obi ya koma kotu da cewar bai kammala wa’adinsa na shekaru hudu ba, lamarin da ya sa kotun koli ta Najeriya ta duba batun ta kuma mayar da shi kan kujerar a ranar 14 ga watan Yunin shekarar 2007.

Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed
Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed

Obi ya nemi wa’adi na biyu a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2010, kuma a ranar 7 ga watan Fabrairu shekarar 2010, hukumar zabe ta kasa ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Bayan kammala wa’adin mulki na biyu, Mista Obi ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, kuma a ranar 12 ga watan Oktoban shekarar 2018, aka ayyana shi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar a lokacin, inda suka zo na biyu a zaben shekarar 2019.

Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed
Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed

A ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2022, Obi ya ayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin tutar PDP a zaben 2023. Amma ya canza sheka zuwa jam’iyyar Labour, inda aka ayyana shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben fidda gwanin da aka gudanar a babban birnin jihar Delta na Asaba a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2022.

Mista Peter Obi mai shekaru 60 a duniya, ya auri Margaret Brownson a shekarar 1992, kuma suna da ‘ya’ya biyu.

Saurari cikakken tarihin cikin sauti:

2023: Tarihin Dan takarar Shugaban Kasa, Peter Obi (LP)- 3'55"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

XS
SM
MD
LG