Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Tarihin Bola Tinubu Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar APC


Asiwaju Bola Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu

An haifi Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Maris a shekarar 1952 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Ko da yake, ba kasafai ake magana akan mahaifinsa ba, amma mahaifiyarsa ita ce shugabar mata ‘yan kasuwa na birnin Legas da ke zaune a Unguwan Tinubu, wanda aka sani da sunan Alhaja Mogajiya Habibat mai arzikin gaske.

Alhaji Bola Ahmed Tinubu da ake wa kirari da Jagaban Borgu, ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya na yankin kabilar Yarbawa.

Tinubu kamar yarda aka fi saninsa, ya fara makarantar sakandare a Ibadan, kafin ya karashe a Kwalejin Richard Daley da ke birnin Illinois a jihar Chicago a kasar Amurka. Bayan ya kamala sakandare ya kuma halarci Jami'ár jihar Chicago inda ya karanci Degree a fannin Akanta tare da kammalawa a shekarar 1979.

Tinubu, lokacin da yake ganawa da Malaman Kungiyoyin Musulmi Na Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya
Tinubu, lokacin da yake ganawa da Malaman Kungiyoyin Musulmi Na Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya

Kafin ya dawo Najeriya, ya yi aiki a kasar ta Amurka a kamfanonin Akanta daban-daban.

Bayan komowarsa gida ne kuma ya shiga harkokin siyasa, inda ya shiga kungiyar People Front ta marigayi Janar Shehu Musa Yaradua, kafin daga bisani su rikide zuwa jamiyar SDP, inda kuma anan ne ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma, tare kuma da samun nasara.

Bayan da sojoji suka soke zaben 12 ga watan Yuni da aka fi sani da zaben Abiola, Tinubu da wasu ‘yan siyasa, musanman daga kudancin kasar, sun tafi gudun hijirah tare kuma da kafa wata kungiya ta ‘yan adawa da mulkin soji mai suna NADECO.

Tinubu tare da shugaba Buhari hagu
Tinubu tare da shugaba Buhari hagu

A yayin da sojoji suka kada gangan siyasa a 1998, Bola Tinubu ya dawo gida, ya tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyar AD ko Alliance for Democracy, inda ya mulki jihar Legas tsawon shekaru takwas.

A wannan lokaci ne dai Tinubu ya kafa abin da ake ganin jam’iyar siyasa da magoya baya da dama da suka zame masa jari a tafiyar siyasarsa ta neman shugabancin Najeriya a wannan lokaci.

Bola Tinubu ya kasance ginshiki wajen ci gaban jihar Legas ta fuskar tattalin arziki, siyasa da kuma abin koyi ga sauran jihohin kasar wajen dogaro da kai da samun kudaden shiga.

Farin jininsa ya karu ne a siyasar Najeriya wajen sunan da ya yi wajen marawa ‘yan Arewa baya a siyasa, tun daga marigayi Janar Shehu Musa ‘Yaradua, zuwa Atiku Abubakar da Nuhu Ribado sai kuma Shugaban Muhammadu Buhari a karkashin jamiyar APC mai Mulki a yanzu.

Lokacin da shugaba Buhari ya ba Tinubu tutar jam'iyya (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Lokacin da shugaba Buhari ya ba Tinubu tutar jam'iyya (Hoto: Fadar shugaban kasa)

Shi ma a bangarensa, Dr. Ahmed Lawal da ke zama shugaban Majalisar Dattijai, na daya daga cikin ‘yan takarar da suka kara da Tinubun a zaben fidda gwani da kuma yanzu yake taya shi yakin neman zabe.

Yanzu haka dai uwargidan Bola Ahmed Tinubu, ita ce Senator Remi Tinubu ‘yar majaisar Dattijai ce mai wakiltar Legas ta Yamma, kuma yana da yaya, kuma daya daga cikin yayansa itace ta gaji sarautar shugabar mata ‘yan kasuwa na birnin Legas daga wajen mahaifiyarsa da ita ma ake kira Habibat Tinubu.

Yanzu dai a yayin da ‘yan Najeriya dama na kasashen wajen suka zura ido domin tunkarar wannan zabe na 25 ga watan Fabrairu, masu iya magana na cewa ba’a sanin maci tuwo sai miya ta kare.

Saurari rahoton Babangida Jibril cikin sauti:

2023: Tarihin Dan Takarar Shugaban Kasa, Bola Tinubu (APC) - 4'30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00

XS
SM
MD
LG