Mahajjatan zasu yini a nan Arafat, domin gudanar da ibada a nan inda Annabi muhammad (saw) ya gabatar da hudubarsa ta karshe, kafin su wuce zuwa Muzdalifa a bayan faduwar rana.
Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe, Injiniya Ibrahim Usman, ya ce a karon farko, dukkan alhazan jihar sun samu zuwa Madinah kafin su taho Makka don damarar fara aikin Hajjin. Haka kuma yace gwamnatin jiharsu ta taimakawa dukkan mahajjatan da kudin sayen ragunan layya.
Su ma alhazai daga Jihar Gombe, sun yaba da irin shirye-shiryen da hukumar alhazan jihar ta yi musu a nan Kasa Mai Tsarki. Wakliliyarmu Sa'adatu Mohammed Fawu da ta tattauna da su, ta ce alhazan sun gama hallara a Mina, kuma da asuba zasu doshi Arafat.