Hajji shi ne aikin ibada mafi dadewa kuma mafi tsarkaka a tarihin addinin Islama, wanda kuma ya wajabta a kan kowane Musulmi, mace da namiji, da ke da koshin lafiya da wadatar arziki. A Makka aka haifi Annabi Muhammad, Sallallahu Alaihi wa Sallam.
Bayan sallar asubahin ranar lahadi, alhazai sun bar Makka zuwa Mina, ta motoci, da jiragen kasa wasu kuma da kafa.
Za su yi salloli a Minna, sannan su huta, kuma a yau litinin su wuce hawan Arfa, inda aka ce a can Annabi Muhammad, Sallallahu Alaihi wa Sallam, Yayi hud'ubar Shi ta karshe.
Gwamnatin kasar Saudiyya ta girke dubban sojoji domin su kiyaye lafiyar alhazai.
Daular Saudiyya mai arzikin man fetur ta dauki manyan matakan, kiwon lafiya da na tsaro domin ta tabbatar da cewa alhazai sun yi zirga-zirga lami lafiya. Haka kuma a cikin shekaru da dama ta kashe dubban miliyoyin daloli domin yin ayyukan gyara da gujewa turereniyar da ke kawo mace-macen alhazai masu dimbin yawa kamar yadda aka yi fama a shekarun baya. Idan ba a manta ba a cikin watan yulin shekarar 1990, an tattake alhazai dubu daya da dari hudu da ishirin da shida cikin turmutsutsu da turereniya.