Shugaban na koriya ta kudu Moon Jae-in ya rubuta wani dan takaitaccen sako ta shafin sada zumuntarsa ranar Lahadi 8 ga watan Nuwamba ya na bayyana goyon bayan sa ga tsohon mataimakin Shugaban na Amurka da mataimakiyarsa Sanata Kamala Harris.
Haka kuma shugabannin kasashen duniya ciki har da Firai Minista Boris Johnson da Shugabar Jamus Angela Merkel sun taya Joe Biden Murna a jiya Asabar bayan da sakamakon kuru’u daga jihar Pennyslvania ya yi hasashen Biden ne ya lashe zaben.
“Amurka muhimmiyar kasar huldarmu ce kuma ina fatan zamu yi aiki tare akan abubuwan da muke ba fifiko, kama daga batun sauyin yanayi zuwa harkokin kasuwanci da kuma tsaro,” a cewar Johnson a wata sanarwa da fadarsa ta fidda.
Wasu magoya bayan Trump sun bayyana bakin cikinsu akan shugabannin kasashen na ketare.
Cikin shugabannin kasashen duniya na farko-farko da suka maida martini akan hasashen cewa Biden ne ya lashe zaben shine Firai Ministan Canada Justin Trudeau.
Facebook Forum