Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu, Gwamnan Zamfara Sun Tattauna Kan Yadda Za’a Magance Matsalar  Tsaro A Jihar


Dauda Lawal
Dauda Lawal

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya gana da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar aso Villa dake birnin Abuja inda suka tattauna karuwar hare-haren ‘yan bindiga da wasu nau’ukan ta’adanci a jiharsa.

ABUJA, NAJERIYA - Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, inda ya bayyana cewa gwamnan ya yiwa shugaba Tinubu bayanin halin da ake ciki na tsaro a jihar Zamfara, musamman yadda ake ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan jihar.

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu da gwamnan sun tattauna dabaru da matakai daban-daban na shawo kan matsalar tsaro da suka hada da inganta matakan tsaro, tattara bayanan sirri da kuma shirye-shiryen hada kai da al’umma.

Ganawar ya kuma jadada mahimmancin bukatar gano tushen matsalar tare da fitar da dabarun magance matsalolin da suka addabe jihar, kamar talauci da rashin aikin yi, wadanda suke cikin ababen da ke taimaka wajen yawaitar miyagun laifuka a jihar.

Haka kuma, a yayin ganawar sirri, Gwamna Lawal ya sanar da shugaban kasa cewa a cikin shekaru 13 da suka gabata, jihar Zamfara ta zama cibiyar 'yan bindiga dake fashi da makami a Arewa maso yammacin Najeriya, in ji sanarwar.

Gwamnan ya kuma roki shugaba Tinubu da ya shiga tsakani da tallafin gwamnatin tarayya wajen samar wa sojoji isassun jami’ai, makamai, da kuma saura kayan aiki taimakawa zirga-zirga domin ba issassu kayan aiki a Zamfara ba, baya ga neman taimako na bangaren sojin sama don taimakawa sojojin kasa.

A wani bangare kuwa, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya baiwa gwamnan tabbacin bada duk wani muhimmin taimako da dabaru ga jami’an tsaro domin tabbatar da maido da zaman lafiya a Zamfara.

Bugu da ƙari, shugaban ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na cewa ba zancen yin sulhu da 'yan ta’adda da kuma biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, ayyukan da ya yi imanin cewa idan ana yi zai rika taimaka miyagun mutanen.

Haka zalika, ana ta rade-raden cewa kasurgumin dan bindiga Dogo Gide ya muta lamarin da wasu al’umomin yankunan arewa maso yamma ke murna da shi.

Idan Ana iya tunawa, a baya-bayan nan ‘yan bindiga sun sace dalibai a yankin Kuriga na jihar Kaduna baya ga yin garkuwa da mutane a wasu sassan Kaduna na daban.

An kuma sake wasu daliban jami’ar gwamnatin tarayya dake Gusau inda ake ci gaba da yin kira ga gwamnati da ta dauki matakan kubutar da dukkan ‘yan Najeriya dake tsare a hannun ‘yan ta’adda.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG