Tun a karshe makon jiya nan 'yan bindag suka ba wa al’umma Batsari wa’adin mako guda ko a zo a ya yi zaman sasanci da su ko kuma su far masu, abin da ya sa al’umma suka ta da hankali domin labarin ya bazu ko ina.
A Najeriya, mahara 'yan bindiga sun dauki wani tsari na mulkin karfi da yaji na tursasa alumomin dake zaune kusa da su cewa dole a yi kaza da kaza in ba haka ba, za su far wa mutane abin kamar almara.
Misali, a makon jiya ne yan ta'adda suka aike da wasika da sako ta waya ga Hakimin Batsari a jihar Katsina dake arewacin Najeriya, suka ba shi wa'adin ya sa a yi zaman sulhu da su in ba haka za su far wa mutanen garin.
Jin hakan ya sa wakilinmu Sani Malumfashi ya bi diddigi, ya je fadar Sarkin Ruwa, wato Hakimin Batsari.
Tabbas Sarkin Ruma, ya ce kwana hudu da suka shige, wani bafillace mai suna Salisu, ya kira shi da waya, bayan sun gaisa sai ya tambaye shi lafiya? Sai Salisu ya ce, ka turo mutanenka sun kashe mana mutane.
Sarki ya ce bai san an kashe kowa ba, amma zai bincika.
Sarkin ya fada wa wakilinmu cewa, wani dan sanda ne ya shiga motar haya tare da wasu 'yan ta'adda sai ya ji suna waya suna cewa ga su nan cikin wata mota mai kama kaza da kaza, dan sanda ya fahimci abin da ke gudana, sai ya hada su da 'yan banga don a bincike su.
Sai aka gane 'yan garkuwa da mutane ne. Ya ce abin da su 'yan bangan suka fada mai ke nan.
Sai ya ce Salisun ya ce ya ba shi kwana bakwai ya sa a yi sasanci, in ba haka za su far musu.
Wakilinmu ya kuma tuntubi Kakakin Rundunar 'yan sanda ta Jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya kuma tabbatar da aukuwar hakan inda ya ce ta kafar sadarwa su ma suka ji cewa ana yadda ta jita-jita cewa 'yan bindiga sun aika da takarda cewa za su zo su dauki fansa.
Sun kuma ji labarin cewa mutanen Batsari sun kame wasu da ake zanton 'yan ta’adan ne, kuma DPO Katsina ya je ya kwashe su amma daga baya mutum biyu sun mutu a asibiti. Wannan fargabar ne ya jawo jita-jitar.
Ya kara da cewa, tuni Kwamishinan 'yan sanda na jihar ya ba da umarni ga mukaddashinsa mai kula da bincike, da a bincika gaskiyar lamarin don a tabbatar ko 'yan ta'adda ne.
SP Gambo Isa ya shawaraci jama 'a da su kwantar da hankalinsu, domin an umarci 'yan sanda da su sa ido da kulawa don gudun abin da ka je ya dawo.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: