Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsegumin Duniyar Fina-Finai na Kannywood


Tesgumi
Tesgumi

A fannin tsegumi kuwa filin DandalinVOA zai tseguntamuku, wata babbar kyauta da wani Hamshakin dan siyasa yayi a babban birnin Kaduna. Shi dai wannan dan siyasan ya baiwa Rashida Adamu Mai-Sa’a, tukwicin mota kirar Marsandi, a dalilin wata waka da ta raira mishi. Ya mika mata wannan kyautar ne a yayin da suka same shi a gidan shi a garin Kaduna, don kaimishi nashi kwafin wakar. Kana kuma baiyi watataba ya kara da bama abokan tafiyarta, guda biyu da kujerun zuwa Hajji, duk a cikin murnar wanna wasashi da mawakiyar tayi.

Shikuwa kamfanin Three Beleivers Media na garin Jos, dake aikin wasu tagwayen fina-finai mai dauke da suna “Bil-Hakki” da “Fasbir” wadanda suke dauke da jarumai kamarsu Ali Nuhu, Tijjani Faraga, Sadiya Adamu, da Maryam But, da dai makamantansu. Wanda Tijjani Maijama’a yabada umurni.

Shikuwa jarimi Yakubu Muhammad, ya kamala kwantirakinshi da kamfanin Intisar Multimedia, wanda suka gabatar da wani fim da akayima lakabi da “Makullin Farko” wanda ke dauke da shahararunan 'yan wasa kamarsu Fati Macijiya, Hanna, Fati Zinariya, Abubakar Gboy, da Feruskan kana da makamantansu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG