Nakasassun sun yi zanga zangar ne har zuwa gidan gwamnatin jihar inda jami’an gwamnatin suka tarbe su.
Da suke gabatar da koken nasu a gaban gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, wanda babban hafsa a gidan gwamnatin jihar Farfesa Maxwell Gidado ya wakilce shi, nakasassun sun koka game da abin da suka kira shakulatin bangaro game da bukatun su.
Daya a cikin shugabannin masu fama da nakasar, ya ce basu je gidan gwamnati da niyar yin zanga zanga ba amma suna jan hankali mahukunta su dubi hali da suke ciki, kana su tuna irin goyon baya da suka baiwa gwamna a lokacin da yake yakin neman zabe a taimakawa musu.
Shugaban kungiyar nakasassu a Mubi, Aliyu Muhammad Abubakar, ya ce sun fara zuwa wurin hukuma ne sun kwaci ‘yancin su. Ya ce akwai masu karatu a cikin su amma abin takaici shine ba a basu aiki kana ba a basu hakkokinsu na tallafin kyautata rayuwa.
To ko me yasa kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka marawa masu bukata ta musamman din a wannan fafutukar da suke yi? Kwamared AbdulSalam Abubakar wani dan rajin kare hakkin dan Adam ya bayyana dalilansu na shiga jerin gwanon.
Ya ce “suna da ‘yanci kamar kowane dan kasa bisa dokokin kasa, dan haka bai yiwuwa a ware wani dan kasa daga cikin wasu abubuwa da ake mora a cikin arzikin kasa saboda yanayin da ya samu kansa a cikin kamar wadannan masu fama da nakasa”.
Da yake mai da jawabi a madadin gwamnan jihar, manzo na musamman da aka aikon, Farfesa Maxwell Gidado ya roke su da su yi hakuri tare da bayyana cewa gwamnatin jihar Adamawa na kokari don share musu hawaye.
Ga dai rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:
Karin bayani akan: jihar Adamawa, Najeriya, da Nigeria.