Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Sace Dalibai 80 A Najeriya Ya Nuna Yadda Rashin Tsaro Ya Ta'azzara


Muhammed Bello, wani yaro da a ka kubutar, baban shi na dauke da shi.
Muhammed Bello, wani yaro da a ka kubutar, baban shi na dauke da shi.

Jami'an tsaro a Najeriya sun kubutar da dalibai 80 a ranar Lahadi, wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Katsina.

An kama daliban ne sannan aka sako su kwanaki kadan da 'yan bindigar suka sako dalibai sama da 300, wanda suka sace har na tsawon mako guda. Yankin dai ya na fuskantar matukar matsalar tsaro.

Mafi akasarin yaran 'yan makarantar Islamiya mata ne, wadanda a ka yi musu kofar rago a karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina. An kama su ne lokacin da suke wani maci na bukin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon Rahama Annabi Muhammad (SA).

Rundunar soji ta ce ta samu nasarar kwato dukkan daliban, har ma da wasu mutane hudu da 'yan bindigar su ka kama a ranar Lahadi, da kuma shanu 12.

Wannan harin ya biyo bayan sace dalibai sama da 300 da aka yi a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, wanda ya ja hankalin kasashen duniya.

Eze Onyekpere, shugaban wata kungiya mai zaman kanta da a ke kira Center for Social Justice, ya ce wadannan hare-haren na kara tabbatar da cewar matsalar tsaro ta wuce kima.

"Wannan ya kara nuna cewar gwamnatin Najeriya ta gaza samar da tsaro, kuma idan aka yi la'akari da alkalumman tantancewa, ana iya cewa Najeriya ita ce kasa da tafi hadari a duniya. Yanzu muna rayuwa ne a inda satar mutane don neman kudin fansa da ayyukan ta'addanci da fashi da makami suka zama wani bangare na rayuwar mu ta yau da kullum," a cewar shi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya na ci gaba da tabbatarwa 'yan kasa cewar zai kawo karshen rashin tsaro a kasar. Ko a makon da ya gabata ya gana da daliban da aka sace bayan an sako su, kuma ya basu kwarin gwiwar cewa ka da su karaya saboda abun da aka yi musu a yanzu.

A dai-dai lokacin da wasu ke yabawa gwamnatin sa na samun nasarar kubutar da yaran cikin sauri, a bangare daya wani masanin harkokin tsaro kuma dan jarida Sanata Iroegbu, ya ce gwamnati na da bukatar sake shiri.

"A duk lokacin da ake da wata matsala sai ka ga an kai sojoji, wannan ba karamin abun damuwa ba ne, wannan ya na kashe karfin jami'an tsaron kasar, don haka wannan yakan kawarda hankalin jami'an tsaron cikin gida. Kamata ya yi sojoji su zama masu tsara yadda za'a magance matsala a cikin gida" a cewar sa.

Ko a wannan watan sai da 'yan majalisar dokokin Najeriya su ka yi kira ga shugaba Buhari da ya sauke hafsoshin tsaron kasar saboda tabarbarewar tsaro.

Onyekpere ya ce ya yarda cewa shugaba Buhari ya na tafiyar hawainiya wajen zartar da abubuwa.

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

"Har sai da ta kai ga cewar ana iya ganin rashin jituwa a shugabancin jami'an tsaron kasar, ba su da nagartar da ya kamata a ce su na da ita, sun gaza kawo karshen wannan yakin da 'yan bindiga". Ya kuma kara da cewar "duk gwamnatin da ba ta iya kare al'ummarta da dukiyoyinsu ba, to ba gwamnati ba ce."

Ko a shekarar 2016 sai da rundunar sojojin Najeriya ta yi ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram a kasar, wanda mafi akasarin hare-harenta, ta na yin su ne a yankin arewa maso gabashin kasar.

Amma masana na ganin cewar kungiyar ta na kara girma, da kuma kara kawance da kungiyoyin 'yan bindiga da suke kama mutane don neman kudin fansa a arewacin Najeriya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG