Gwamna Zulum ya bayyana haka ne da yake tsokaci kan halin da matafiya ke ciki a jihar Borno da kuma sauran jihohin kasar.
"Jami'an sojin Najeriya sun gaza kare matafiya" wannan babban abun takaici ne, aga wannan munmunan aika-aikan na faruwa a kan hanyar zuwa garuruwan Sakana da Auno, garuruwan da ke da tazarar kilomita 20 kacal. A cewar Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum.
Abun ban mamaki akwai jami'an tsaro da aka girke a kan hanyar, daban da ban, amma basa aikin su yadda ya kamata. Sai dai ka gansu sun kafa shinge don karbar kudi daga hannun matafiya.
Kuma sannin kowa ne an dauke su aiki ne don kare lafiyar 'yan kasa, amma babu abun da yafi ci musu tuwo a kwarya na rashin ganin wadannan jami'an suna aikin da aka dauke su akai.
Farfesa Zulum da tafi ya zuwa Auno ya bayyana cewa, "banga jami'in tsaro ko daya akan hanyar ba, don haka ya kamata gwamnatin tarayya da rundunar tsaron kasa dole ne su saurari kukan al'umma, da kuma sanin wane irin hali wadannan jami'an nasu ke ciki, don daukar matakai da suka dace na ladabtar da su, idan aka samu mutum da karya dokar aikin da aka dauke shi yayi.
Gwamna Zulum ya kara da cewar, an kona motoci da dama akan hanyar, wasu kuma sun rasa rayukan su, wasu kuwa dukiyoyin su. Wani mutum da ya kubuta, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, 'yan ta'addan sun tare su, inda suka shiga daji don neman tsiratar da rayukansu, mutumin ya kara da cewar yana ji yana gani 'yan ta'addan suka tafi da yarinyar shi da suke tare.
Saurari rahoton Haruna Dauda Biu a cikin sauti.