Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sokoto: Mahaifi Ya Bayar Da Umarni An Kashe Dan Sa


Motocin 'yan Sanda.
Motocin 'yan Sanda.

Lokacin da yan Najeriya ke fuskantar matsalolin satar mutane da kisan gilla daga ‘yan bindiga, wani mahaifi a jihar Sakkwato umurni ya bayar aka kashe Dan sa na cikin sa.

Lamarin ya faru ne a wani kauye da ke Kibiyare cikin karamar hukumar Yabo a jihar Sakkwato, inda wani mahaifi mai suna Umaru ya umurci ‘ya 'yansa biyu su kashe Dan sa daya mai suna Abubakar Kuma suka kashe shi, mahaifin ya ce ya gafarta musu.

Duk da yake mahaifin tare da yaran na sa biyu da suka yi wannan aika-aikar suna hannun hukumar ‘yan sanda, jami'in tsaro na banga mai suna Muhammad Dan kurma wanda shi ganau ne, shi ne ya kama mutanen kafin ya mika su ga hukuma.

A karamar hukumar Goronyo kuma, har yanzu mutane na zaman zullumi, domin har yanzu ‘yan bindiga na yiwa jama'a kisan dai dai, kamar yadda ya faru a karshen mako.

A karamar hukumar Tangaza, ‘yan bindigar sun kai farmaki inda suka hallaka wani mutum Alhaji Isa sarkin bakin Tangaza.

Lamarin satar mutane da kisan dauki dai dai da ake yiwa jama'a a Najeriya, yana ci gaba da kazancewa abin da ya karkata hankulan wasu ganin ya kamata a koma wa Allah domin neman mafita.

Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00


Karin bayani akan: Sokoto, jihar Sakkwato​, da 'yan Sanda.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG