A matsayina na shugaban rundunar sojojin Najeriya, na umurci sojoji dake bakin daga da kada su daga kafa har sai sunga bayan wadanan miyagun, da ke addabar jama'a wajen satar mutane don neman kudin fansa.
Don ganin an kawo karshen wannan matsalar, Burutai, ya kara wa'adin aikin dakarun da suke aiki don kawo karshen wadannan miyagun, daga nan har zuwa watanni ukku na farkon sabuwar shekara. Karin wa'adin yazo ne a dai-dai lokacin da hare-haren miyagun yake kara hauhawa, don haka muna ganin idan aka kara shi zamu iya samun nasarar murkushesu nan bada jimawa ba, a cewar Burutai.
Dr. Kabir Adamu, masani a fannin tsaro, yana ganin cewar, tun ba yau ba ya kamata a dauki kwararan matakai don mamaye dokar dajin, ana iya cinma wannan idan an yi amfani da na'urorin zamani, musamman wajen amfani da jirage masu saukar angulu. Idan aka yi la'akari da kasashen da suka cigaba a duniya, sukan yi amfani da waddanan na'urorin wajen magance matsaloli da suke cikin dokar daji.
A wannan karni na 21 da ake ciki, ana iya amfani da na'urar tauraron dan adam, wajen ganin ina ne makwantar wadannan miyagun don yin farautar su, da tarwatsasu cikin kankanin lokaci. Akwai bukatar rundunar sojojin Najeriya ta sanar da al'ummah irin matakai da suke dauka don yaki da wadannan miyagun.
Win kwamanda Musa Isa Salmanu, wanda ya ke masani kan aikin soji, ya ce dama dai shi soja ba'a sanshi da aiki na zama waje daya ba, akan bashi wa'adi mafi karanci don gudanar da aiki, wanda ta haka zai iya gabatar da aikinsa yadda ya kamata.
Ya kara da cewar a lokacin yaki, akan yi amfani da jami'an tsaro daban-daban, akwai lokacin da sojoji ke taka rawa, kuma ana iya kaiwa wani lokaci da sojoji zasu baiwa 'yan sanda wuri, haka suma ana iya kaiwa lokacin da aikin su kan kare, a wannan lokacin akwai bukatar kawo jami'ai dake da kwarewa a wannan yanayin.
Salmanu ya ce, rashin gazawar wasu manya a gidan soji ne yasa kake ganin a kowane lokaci akan kai sojoji don yaki a kowane irin hali, ya kamata a dinga duba irin yaki da kowane jami'an tsaro ke da kwarewa, da kuma sanin cewar zasu iya, ba kawai a kowane lokaci a dinga kai sojoji yaki ba, har wanda basu da kwarewa akan shi.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina a cikin sauti.
Karin bayani akan: sojojin Najeriya, sojoji, Janar Tukur Yusuf Burutai, da Nigeria.