Kasaitacen taron da za'a yi a Abuja ya samo wakilai daga kowane sakon kasar. Wajen 'yan siyasa dubu shida da dari takwas da hamsin da biyar ne zasu halarci taron a dandalin nan na Eagle Square. Daga cikin mahalartan ne za'a fitar da shugabannin jam'iyyar na kasa baki daya.
Tun kafin a kawo wannan lokacin sai da kusoshin jam'iyyar suka yi wani kasaitacen taro inda suka tafka muhawarori da shawarwari domin a samu matsayi akan yadda za'a rarraba mukamai zuwa kowane yanki na Najeriya.
A tsarin da suka amince dashi da kuma za'a yi anfani dashi a taron shugaban jam'iyyar zai fito daga yankin kudu maso kudun kasar. Arewa maso gabashin kasar zata samu babban sakatare.Kudu maso yammacin kasar zata bada mataimakin shugaban jam'iyya na kasa.Kudu maso gabashin kasar zata fitar da mataimakin babban sakatere. Arewa ta tsakiya zata fitar da sakataren watsa labarai. Arewa maso yamma zata fitar da mataimakin shugaban jam'iyyar.
A jerin wadanda suka halarci taron da ya fitar da tsare-tsaren har da na rarraba mukamai kusoshin jam'iyyar sun amince.Kamar yadda shugaban tsare-tsaren ya bayyana wato gwamna Magatakarda Wamako na Sokoto zabe za'a yi. Babu batun daidaitawa. Walikan taron su ne zasu yi zaben duk mukaman da aka zana.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.