Girgizar kasa, da aman wuta da kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya na iya janyo mummunan zaftarewar tsaunuka da laka. Zaftarewar laka na iya ragargaza duk wani abu da ta ci karo da shi.
Da taimakon na’urorin tauraron dan adam masu karfi, masana kimiya na zana wuraren da ake samu ko za a iya samun zaftarewar laka, da zummar taimakawa wuraren da bala’in ya shafa iya yin hasashen inda ko wurin da zaftarewar za ta iya faruwa. A cewar wani rahoto da George Putich na Muryar Amurka ya hada.
A kowacce shekara zaftarewar laka na janyo asarar kaddarori da rayuka dayawa, musamman a yankuna marasa galihu.
Cibiyar nazarin sararinsamaniya ta kasa da ake kira NASA a takaice ta ce, yawancin lokuta zaftarewar laka na faruwa ne a lokacin da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya jika laka sosai akan tudu, a hankali sai kasar ta zaftare. Amma za ta iya faruwa sanadiyar girgizar kasa, ko zaizayewar kasa, ko hakar kasa.
Masanin kimiya Thomas Stanley da kungiyar jami’oin binciken sararin samaniya, tareda hadin guywar cibiyar NASA, sun yi nazarin dangantakar dake tsakanin ruwan sama da zaftarewar kasa, yayinda suke kokarin fidda cikakkiyar taswirar wuraren dake tattare da hadarin bala’in.
Thomas ya ce, abin nufi a nan shine, idan aka sami ruwan sama da ya wuce kima, za mu iya cewa zaftarewar kasa na iya faruwa a wani wuri.
Facebook Forum