A ranar Asabar da ta gabata ne hukumar binciken sararrin samaniya ta Amurka NASA, ta harba wani jirgin Roket zuwa duniyar sama, daga sansanin sojojin sama dake jihar California. Babban makasudin aika jirgin duniyar, don ganin yadda tsarin duniyar yake, duniyar da akayima lakabi da “Red Planet”
Wannan jirgin shine kirar farko da hukumar ta taba kirkira don gudanar da wannan aikin, jirgin kirar Atlas 5, zai yi tafiya da ta kai kimanin kilomita milliyan dari hudu da tamanin da hudu, kamun isa duniyar ta red planet.
Ana sa tsanmanin jirgin ya isa duniyar wanda zai yi tafiyar kimanin watanni shida, inda zai sauka kusa da wani yanki da ake kira ‘Elysium’ mai kimanin tafiyar kilomita dari shidda, da nisan inda aka shiryar da mota mai tuka kanta zata sauka a shekarar 2022 idan Allah ya kai rai.
Masana sun bayyanar da wannan a matsayin wata tafiya dake tattare da abubuwan al’ajabi, domin kuwa sun hango kadan daga cikin irin yanayin duniyar, tana zagaye da wasu marafai masu kama da yadda albasa take, suna sa tsanmanin tafiyar ta bayyanar da wasu abubuwa na ban mamaki a duniyar ta sama.
Facebook Forum