A makon da ya gabata ne masana’antar Kannywood ta yi babban rashin Jaruma Hauwa Maina, wacce ta rasu a yammacin ranar labarar da ta gabata.
Akan haka ne DandalinVOA ya samu zarafin zantawa da jami’n hulda da jama’a na kungiyar masu shirya fina-finai ta MOPPAN reshen jihar Kano Murtala Balarabe Baharu.
Hauwa Maina, ta shiga masa’antar fim tun 1999 inda ta fara da wani fim mai suna Tuba, a matsayin jaruma, kuma a mafi yawan fina-finan ta, ta fi mayar da hankali ga bangaren da ke nuna jajircewar diya mace.
ya ce Hauwa Maina, mace ce da ta shiga masana’antar fim da iliminta inda tana daga cikin matan da ke masana'antar da ba a dar-dar wajen taka duk irin rawar da aka bukace su su taka.
Ya kara da cewa a wasu lokutan ma marigayiyar takan fito a wasu fina-finan Hausa da aka fitar da su a harshen turanci, daga ciki har da wani Fim mai suna 'DRY' wanda ta samu lambar yabo a fim din da aka yi a harshen Turanci, sai fim din There is a Way’ na kamfanin Jammaje.
Daga karshe ya bayyana cewa Hauwa Maina mace ce mai karbar fina-finan da ke dauke da nasiha ko sakonnin ilimi da sauran su, ya ce masanaantar Kannywood dai tayi babban rashi da samun wacce zata maye gurbinta abu ne mai wuyar gaske.
Facebook Forum