Wasu na danganta hakan da faduwar darajar Naira, wasu kuma na ganin cire tallafin man-fetur ne babbar sila, a gefe guda kuma wasu na alakanta hakan da yake-yaken Rasha da Ukraniya da kuma Isra'ila da Falasdinu.
Sai dai wasu kuma na ganin yan kasuwa ne ke tunzura hauhawar farashin wajen boye kayayyakin domin cin kazamar riba.
A hirarsa da wakiliyar Muryar Amurka, Rukaiya Basha, Dakta Isa Abdullahi Kashere, masani kuma Malamin Tattalin Arziki a Jami'ar Tarayya ta Kashere dake jihar Gombe, ya yi tsokaci game da ababen dake tunzura hauhawar farashin kayaki da kuma faduwar darajar Naira a kasar.
Yanzu dai hankulan ƴan kasar ya karkata ne ga gwamnatin tarayya, domin ganin yadda sabbin matakan da ta dauka zai kawo saukin lamura.
Ga cikakken hiran Rukaiya Basha da Dakta Isa Abdullahi:
Dandalin Mu Tattauna