Gwamnan ya bada wannan umarni ne a ranar Alhamis sa’ilin da yake martani ga gagarumar zanga-zangar data barke a babban birnin jihar Minna, akan hauhawar farashi da matsin tattalin arziki da ake fama dasu a najeriya a halin yanzu.
A cewarsa, jita-jitar cewa gwamnatin na shirin boye kayan tallafin abinci a jihar duk da tsananin yunwar da jama’a ke fuskanta ce ta haddasa zanga-zangar.
A ranar Laraba ne Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mata guda uku da ake zargin suna da hannu wajen shirya zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a jihar Neja a ranar Litanin din nan da ta gabata.
Wata sanarwa daga Kakakin ‘Yan Sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ta nuna sun kama wata Aisha Jibrin mai shekaru 30 da suka ce ita ce ta tsara yadda aka gudanar da wannan zanga-zangar.
Sauran matan sun hada da Fatima Aliyu yar shekaru 57, da kuma Fatima Isyaku mai shekaru 43. Ko baya ga wannan dai ‘yan sandan sun ce sun kama wasu matasa 24 da suke zargin suna da hannu wajan shiga wannan zanga-zanga.
In ba a manta ba, jiya ne Mohammed Idris, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a ya ce matsalar karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da ita a kasar hade da kunci rayuwa ya sa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin sakin shinkafa da masara tan dubu 102,000 ga ‘yan Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta kuma ja kunnen masu boye abinci, inda tayi kira ga jama’a su nuna kishin kasa a halin da ake ciki, ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya a shirye take ta zartar da hukunci kan musu boye abincin.
Matakin dai ya biyo bayan zanga-zangar da ‘yan Najeriya suka yi kan tsadar abinci da sauran kalubalen tattalin arziki.
Dandalin Mu Tattauna