Shugaban Hukumar, Barista Muhyi Magaji Ramingado, wanda ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a Kano, yace hukumar na tattara bayanan sirri akan batun kuma tana shirin afkawa irin wadannan dakunan ajiya da sito-sito kannan da azumin watan ramadan.
Ya kuma bukaci al’umma dasu taimakawa hukumar da bayanan da zasu taimaka mata wajen gano irin wadannan dakunan ajiya da sito-sito.
Ya kara da cewar: “duba da tunkarowar azumin watan Ramadan, baza mu nade hannuwa muna kallon al’amura na ta’azzara ba, zamu dau matakin gaggawa. baza mu bari wasu suyi amfani da wannan dama ta hanyar boye kayan masarufi domin kara ta’azzara halin da ake ciki ba.”
“Muna kira ga mutanen dake da muhimman bayana dasu fito su taimakawa hukumarmu ta gano wuraren da ake boye kayan masarufi. hakan zai farantawa hukumarmu rai kuma ba zata fallasa bayanan irin wadannan mutane ba.”
“Na san akwai matsalar hauhawar farashi wacce ta kasance ummulhaba’isin halin kuncin da ake ciki saidai batun boye kayan masarufi ma ya taimaka. saidai ba zamu kyale hakan ta ci gaba ba”, a cewarsa.
Dandalin Mu Tattauna