Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Boko Haram Yace Sune Suka Kai Farmaki a Kan Sansanin Soja a Maiduguri


Abubakar Shekau
Abubakar Shekau

Abubakar Shekau ya bayyana wannan cikin wani faifan bidiyo na tsawon minti 40 da kungiyarsa ta fitar ta hannun 'yan jarida na Najeriya jiya alhamis.

Shugaban kungiyar nan ta Boko Haram a Najeriya yace kungiyarsa ce ta kai hari a kan wani sansanin sojan Najeriya a cikin wannan watan a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Abubakar Shekau shi ya bayyana wannan a cikin wani faifan bidiyo mai tsawon minti 40 wanda aka fitar ta hannun 'yan jaridar Najeriya alhamis din nan.

Shekau yace Allah Ya ba kungiyarsa abinda ya kira “nasara” a wannan farmaki da suka kai a kan sansanin sojan na Maiduguri, cibiyar wannan kungiyar kishin Islama wadda ba a san cikakkiyar aniyarta ba.

A ranar 2 ga watan Disamba, 'yan bindiga sun kai farmaki a kan wani sansanin mayakan sama, da wani barikin soja a kusa da nan, duka a garin na Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya.

Wani kakakin ma'aikatar tsaron Najeriya yace an kashe 'yan Boko Haram su 24 a musanyar wuta da sojoji a wannan sansani. Sai dai bai ce ko an kashe wani soja ko kuma farar hula ba.

Wata wakiliyar VOA da ta ziyarci inda aka gwabza fada a bayan harin ta ce an yi barna sosai a barikin sojan da kuma wani caji ofis na 'yan sanda dake kusa da nan.

Har ila yau a cikin wannan faifan bidiyo, Shekau ya sake gargadin cewa kungiyarsa zata kai farmaki a kan Amurka.
Wani dan jarida da ya ga bidiyon yace Shekau ya sanya kaki irin na soja, yana rike da wata bindiga mai kama da kirar Rasha, kuma a wasu lokuta yana nuna hali na tsananin jijjiga ko zafi a maganarsa.

Yayi magana a cikin harsunan Larabci, Hausa da Kanuri. Sauran abinda ke cin bidiyon da alamun sassa ne na farmakin da tsageran suka kai a kan sansanin sojan na Maiduguri a farkon wata.

Har yanzu ba a tabbatar da sahihancin wannan faifan bidiyo ba.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG