Kwanaki biyu bayan harin da wadansu yan ta'adda suka kai garin Midale a jamhuriyar Nijar ga jami'an tsaro, yanzu dai kwanciyar hankali ya dawo a wannan yankin inda gwamnati ta karfafa matakan tsaro yayinda kuma masu rajin kare hakkin dan Adam ke kira ga ‘yan Nijar da su kara ba askarawan kasar goyon baya.
Gwamnatin ta jamhuriyar Nijar, tayi kira ga jama’ar kasar dasu bada hadin kai domin a samu a shawo kan wannan matsalla ta tsaro domin a cewar gwamnati matsallar tsaro matsalla ce wace ta shafi kowane dan kasa.
Haka ma a garin Tchin Tabaraden, wani dan jarida Malam Sidi Muhammad, dake yankin yace gwamnatin jamhuriyar Nijar, ta dauki dukan matakan da suka wajaba domin tabbatar da kwanciyar hankali a wannan yankin
A nasa bangaren shugaban kungiyar Karen hakkin dan Adam, Abdullahi Ka’do, yace ya kyautu ‘yan Nijar su kara tabbatar da goyon bayansu ga jami’an tsaron kasar akan wannan jan aiki da suke yin a yaki da ‘yan ta’adda.
Ya kara da kira ga gwamnatin kasar da ta sake dawo da gidauniyar da kade Kaden karfafawa jami’an kasar Nijar gwiwa domin su samu cimma burinsu na tarwatsa ‘yan ta’addan da suka addabin yankin mu.
Facebook Forum