An yi kira ga kabilu da ke fada da juna mazauna yankin tsaunin Mambila na karamar hukumar Sardauna dake jihar Taraba kada su yi sake wasu su rika ingizawa da ruruta kyama sakaninsu don haddasa tashe-tashen hankula a yakin.
Wannan na kunshe a cikin yarjejeniyar da mahalarta taron wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwar kungiyar mabiya addinin Kirista da majalisar gamayyar kungiyoyin addinin Musulumci ta gudanar a Gembu biyo bayan tashe-tashen hankula da yankin ya yi fama das makonni da suka gabata.
Shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista ta kasa reshen jihar Taraba Rev. Dr, Ben Ubeh wanda ya karanta jawabi bayan taron mai kudurori biyar yace kowace kabila na da yancin walwala da sarrafa albarkatu da Allah ya wadata yankin dasu.
Rev. Dr, Ben yace sun yi Allah wadai da wadanda suka haddasa wadannan ayuka na ta’addanci da nuna bukatar a hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki kana da jajantawa wadanda suka yi asarar ‘yan uwa da dukiyoyinsu.
Bakin shugabannin addinan biyu ya zo daya kan batun akwai wasu da ke ingiza rikicin da yake abkuwa daga waje tare da gargadin su bukaci irin wadannan mutanen da iyalansu su yi masu jagora a duk lokacin da suka nemi haddasa tashin hankali kamar yadda shugaban majalisar gamayyar kungiyoyin addini Musulumci ta kasa reshen jihar Taraba Alhaji Inuwa Usman Mafindi da takwararsa suka yi bayani.
Su ma Imam Mustapha, Ambasada Rabecca Anthony da Grand Khadi Ahmed Mahmudu daga cikin wadanda suka halarci taron sun bayyana wa Muryar Amurka cewa taron wani tUbali ne na kyautata fahimtar juna, kawar da kyama da maido da zaman lafiya.
Sai dai mahalarta taron sun bukaci gwamnatocin tarayya da na jihar Taraba su tsananta tsaro a kauyuka dake kewaye don dakile masu niyyar kai harin ramuwar gayya.
A saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum