Gwamnatin Najeriya ta ce ta na da shirin kafa wata hukuma ta musamman da za ta rika tattara kudaden da aka kwato daga hannun wadanda suka sace kudaden kasar.
Ministan Shari'a kuma babban Atoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami ne ya bayyana hakan, bayan da wata kotun tarayya a jihar Legas ta yanke hukunci a jiya Laraba cewa gwamnati ta yi "maza-maza" ta bayyana sunayen wadanda suka sace kudaden kasar.
Har ila yau kotun ta nemi gwamnatin ta tarayya da fadi adadin kudaden da aka tattara ya zuwa yanzu.
Kungiyar SERAP mai fafitukar ganin an yi adalci kan harkokin da suka shafi tattalin arzikin kasa ce ta shigar da karar a gaban kotu.
A kuma jiya Laraba mai Shari'a Hon. Hadiza Rabiu Shagari ta yanke hukuncin cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Professor Yemi Osinbanjo su bayyana sunan wadanda suka sace kudaden Najeriya, su kuma bayyana nawa aka kwato ya zuwa yanzu.
Saurari rahoton da wakilin Nasiru Adamu El Hikaya ya hada mana kan tsokacin da gwamnatin Najeriya ta yi kan hukuncin kotun.
Facebook Forum