Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yiwa Alfaga Zakaran Taekwondo na Duniya Gagarumar Tarba a Nijar


Zakaren wasan Taekwondo na Duniya Abdurazak Issoufou Alfaga
Zakaren wasan Taekwondo na Duniya Abdurazak Issoufou Alfaga

A Janhuriyar Nijar daruruwan 'yan kasar ne suka tarbi sabon Zakaren wasan Taekwondo na Duniya Abdurazak Issoufou Alfaga ,bayan kammala gasar Teakwondo ta Duniya da aka gudanar a makon da ya gabata a kasar Koriya ta Kudu.

Wadanda suka halarci bukin tarbar dan wasan sun bayyana cewa, banda kasancewarshi dan asalin kasar, dan wasan ya kuma zama gwani a duniya baki daya wanda kasashen nahiyar Afrika baki daya zasu yi alfahari da shi.

Wani mai sharhin a kan lamura ya bayyana cewa, rabon Jamhuriyar Nijar ta sami irin wannan nasarar tun zamanin Isiyaka Dabore, amma gashi yau dan wasan ya daga tutar kasar.

Wani matashi mai wasan barkwanci a Jamhuriyar Nijar, yace wannan nasarar zata karawa matasa karfin guiwa dake sha’awar fitar da sunan kasar a waje. Suka kuma yi kira ga gwamnati su kara bashi goyon baya da kuma dukan ‘yan asalin kasar da suke da basira da kuma gurin yin fice.

A nashi tsokacin, zakaran Taekwondo na Duniya Abdurazak Issoufou Alfaga ya bayyana farin ciki ganin irin tarbar da aka yi mashi da yace zata kara mashi karfin guiwa a wasanni na gaba.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Yusuf Abdullahi ya aiko mana daga birnin Yamai.

Tarbar Zakaran wasan Taekwondo na Duniya -3'19
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG