Wakilin Amurka a wurin tattaunawar cinikayyar, Robert Lightizer, yace tattaunawar Amurka da Canada zata ci gaba a ranar Laraba kuma yace akwai yiwuwar Canada zata karu a cikin shirin cinikin kasashen Arewacin Amurka da shugaban kasa zai sanya hannu akai a cikin watan Nuwamba.
Mai wakiltan Canada a wurin tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar, Chrystia Freeland, ta bayyana kwarin gwiwarta cewa kasashen zasu cimma daidaito da zai amfani bangarorin guda biyu.
Freeland ta fadawa manema labarai cewa akwai yiwuwar cimma yarjejeniya mai amfani ga kowane bangare, bayan tattaunawarsu da Lightizer a nan Washington.
Sai dai hira da sashen labaran telbijin Bloomberg ya yi da shugaba Trump ta dauke hankali fiye da tattaunawar cinikayya tsakanin Canada da Amurka din.
Facebook Forum