ACCRA, GHANA -Manoman kokon a garin Gyampokrom da ke gundumar Sefwi Juaboso da ke yankin Arewacin Ghana sun yi barazanar fitar da kayan kokon zuwa kasar Ivory Coast idan gwamnati taki kara farashin koko ta shekara 2022 da 2023.
Inda suka bukaci gwamnati ta kara kudin buhun koko daya , wanda a halin yanzu ake sayar dashi akan ¢660.00, kwatankwacin dalar Amurka 63$ zuwa ¢1,200.00. Kwatankwacin dalar Amurka $126.
A cewar manoman, su ma matsalolin tattalin arzikin kasar da ake ciki a halin yanzu ya shafe su. Saboda farashin kayan yin aikin gona, da ma'aikata da sauran ayyuka duk sun tashi
Shugaban kungiyar manoman yankin Issifu Issaka ya ce, suna kira ga gwamnati da ta taimaka ta kara farashin koko zuwa kaso 30 cikin dari.
Saboda suna girbe koko mai yawa a wannan yanki amma babu wani amfani da suke samu daga aikinsu. Suna yin ayyukan noma a bangarori daban-daban duk da haka, ba su iya biyan kudin karatun ’ya’yansu.
Ya ce sun ji cewa kasuwancin koko yana tashi kuma akwai riba sosai a kasar Cote d'Ivoire don haka idan gwamnati ba ta kara musu farashi ba, za mu fitar da kokon zuwa kasar waje, domin kuwa cikin sa’a yankinsu yana kusa da iyakar Ivory Coast.
A cikin yunkurin kara farashi ko kaso, Hukumar CocoBod za ta amince da wannan matakin neman kara farashin koko, saboda CocoBod bata da alhakin kara ko rage farashi, saidai kwamitin samar da koko a Ghana su zasu iya sake farashi.
Saurari cikakken rahoto daga Hawa AbdulKarim: